fbpx
Monday, June 27
Shadow

Kotu ta yankewa wani manomi hukuncin shekaru 10 a gidan yari bayan ya yiwa wata yarinya fyade kuma ya zaneta saboda bata masa lokaci datayi

Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani mutun mai suna Tobi Owajulu hukuncin shekaru 10 a gidan yari bayan daya yiwa wata yarinya ‘yar shekara 17 fyade.

Yarin ta bayyana cewa a ranar taje gonar kakarta ne domin girbo kayan da suka shuka sai mutumin yace mata ta bashi ruwa da ‘ya ‘yan itace. Sai tace mata ba ruwa kuma ‘ya ‘yan itacen na kakarta ne.

Can bayan wasu lokuta sai ya dawo ya rikota ta baya ya rufe mata baki da kaya ta kasa yin ihu kuma yayi nasarar afka mata, sannan kuma ya zaneta saboda ta bata masa lokaci.

Karanta wannan  An damke mutumin daya kashe wata mata mai yara biyu a jihar Anambra

A hanyarta na dawowa ne ta hadu da wasu mutane suka kaita asibiti bayan da suka ganta tana kuka kafin aka sanar da iyayenta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.