fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari bisa laifin fashi da makami

Mai shari’a Hakeem Oshodi na wata babbar kotu da ke Ikeja ya yanke wa wani mutum Shola Agboola hukuncin daurin shekara 21 a gidan yari bisa laifin fashi da makami.

Jastis Oshodi a ranar Alhamis ya yankewa Agboola hukuncin ne bayan an same shi da laifuka guda uku da gwamnatin jihar Legas ta gabatar a kan sa mai lamba ID / 706c / 14.

Tun da farko ‘yan sanda sun cafke mai laifin kuma Gwamnatin Jihar ta gurfanar da shi a ranar 3 ga watan Agustan 2014, kan tuhume-tuhume hudu da suka hada da fashi da makami, hada baki don yin fashi da cin zarafi a kan wasu mutane biyu.

Lauya mai shigar da kara, Olabisi Ogungbesan, na Daraktan shigar da kara na jama’a (DPP), Ma’aikatar Shari’a ta Jihar, ya bukaci kotun da ta hukunta Agboola kamar yadda ake tuhumarsa saboda girman laifukansa.

A yayin shari’ar, mai gabatar kara gabatar da shaidu hudu da kuma wasu biyar a gaban kotun.

Da yake yanke hukunci a kan lamarin, Mai shari’a Oshodi ya ce shaidun da masu gabatar da kara suka bayar tabbatattu ne kuma masu gamsarwa.

Mai shari’a Oshodi ya samu wanda ake tuhumar da laifi kamar yadda ake tuhumarsa kuma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari.

Alkalin yace, ya yanke hukuncin ne kamar yadda sashi na 297, 295 (2a) da 172 na dokokin manyan laifuka na jihar Legas ta shekarar 2015.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *