fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Kotu ta yankewa Yunusa Yallo hukuncin shekara 26 a gidan yari

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a garin Yenagoa na jihar Bayelsa ta yankewa Yinusa Dahiru hukuncin wanda aka fi sani da Yunusa Yello daurin shekara 26 a gidan yaria.

Ana zargin sa ne dai da sace wata yarinya ‘yar asalin jihar ta Beyelsa, Ese Oruru, sannan ya aure ta ba tare da amincewarta ba, kodayake ya sha musanta zargin.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara.

Kotun karkashin jagoranicn Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Dahiru shekaru 26 a gidan yari kan laifuffuka  biyar.
Idan zaku iya tunawa Yunusa ya gudu da Oruru daga jihar bayalsa inda ya taho da ita zuwa jihar Kano a ranar 12 ga watan Ogusta a Shekarar ta 2015, inda kuma ya aureta tare da musuluntar da ita wanda ta kai sun samu karuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *