Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar neman belin tsohon gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya jagoranci zaman a ranar Juma’a, bayan sauraron bukatar lauyan Rochas, Ola Olanipekun.
Lauyan ya nemi kotun ta bayar da belin, na wani dan lokaci kuma na talala zuwa kan a gabatar da binciken EFCC.
Ekwo ya dage zaman kotu zuwa ranar 30 ga watan Mayu, ranar da za a saurari kararsa da EFCC ta shigar.
A ranar 25 ga watan Mayu EFCC ta kama Okorocha a gidansa da ke Abuja, suna ikrarin cewa ya karya belin da aka bayar a kanshi tun da farko.