Kotu a jihar Ekiti ta yankewa wani dansanda, ACP, Akubo Aboye hukuncin daurin rai da rai a gidan yari saboda samunsa da sayen motar sata daga hannun masu garkuwa da mutane.
Hakanan kotun ta daure wasu mutane 7 da aka samu da laifin satar mutane dan kudin fansa tsawon shekaru 5 ba tare da dsmar biyan diyya ba. Wanda aka daure din sune,
Solomon Ayodele Obamoyegun (39), Femi Omiawe (40), Damilola Obamoyegun (20), Bose Sade Ajayi (30), George Lucky (35), Chukwuma Nnamani (22) da Sunday Ogunleye (45).
Yansanda masu Bincike sun bayyana cewa binciken ya kaisu suka gano motar satar a cikin gidan ACP Akubo inda kuma ya amsa laifin cewa ta hannun makanikensa ya sayi motar.
“I found you guilty of receiving stolen vehicle. All evidence pointed to the fact that you were aware that the car was stolen. You are hereby sentenced to life imprisonment for the offence,” he said.