Karar da tsohon gwmanan jihar Rivers, kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shigar yana neman kada a a binciki yanda yayi mulkin jihar Rivers na tsawon shekaru 8 bata yi nasara ba.
Kotun Allah ya isa dake Abuja tace Amaechi bai bayar da wata hujja data gamsar da ita ba da zata hana a bincikeshi kan zargin satar kudin ba.
Kotun ta kuma kara da cewa, dan haka Amaechi ya je ya amsa zarge-zargen da ake masa.
Ana zargin tsohon gwamnan ne da sayar da wasu kadarori mallakin jihar ta Rivers, inda yayi sama da fadi dasu.
Amaechi dai na daga cikin wanda suke neman samun tikitin takarar shugaban kasa na shekarar 2023 karkashin jam’iyyar APC.