fbpx
Friday, August 12
Shadow

Kotu tayi watsi da karan bayar da belin shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

Babbar kotun tarayya da ke Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan a-ware ta Biyafara, (IPOB), Nnamdi Kanu.

A lokacin da take yanke hukuncin a yau Talata, Mai shari’a Binta Nyako, ta ce bukatar aba ce da ke zaman cin zarafi ga shari’a, kuma yunkuri ne na ci gaba da magana a kan abin da aka riga aka yanke hukunci a kai.

Sai dai ta shawarci wanda ke neman belin da ya nufi kotun daukaka kara a kan batun, idan bai gamsu da hukuncin ta ba.

Karanta wannan  Yadda Barcelona ta sayar da kadarorinta ta sayo sabbin 'yan wasa a wannan kakar

Mai shari’ar ta ce tun bayan da aka yanke hukunci a watan Yuli na 2017, lokacin da aka bayar da belin Kanu zuwa yau, an daga shari’ar har sau 15, kuma har yanzu ba a kai ga sauraren ainahin shari’ar tasa ba ma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.