fbpx
Friday, December 2
Shadow

Kotun ɗaukaka kara ta dawo wa Aishatu Binani takararta ta gwamna

Wata kotun ɗaukaka kara a birnin Yola na Adamawa ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halastacciyar ‘yar takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC.

Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan ya jagoranta ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ya sauke takarar Aishatu Binani, da sanar da cewa APC ba ta da takara a zaɓen 2023.

A lokacin sanar da hukuncinsa, alkalin ya umarci a miƙa sunan Binani ga hukumar zaɓe mai zamanta wato INEC, a matsayin ‘yar takarar gwamnan APC a Adamawa.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *