fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Kotun daukaka kara ta yankewa wata mata hukuncin shekara 34 kan amfani da Twitter a Saudiyya

Kotun daukaka kara ta yankewa wata mata yar shekara 34, Salma al-Shehab hukuncin shekara 34 a gidan yari kan amfani da Twitter datayi ba bisa ka’idar kasar ba.

Matar tana yada labarai ne akan nemawa matan saudiyya hakkin su na walwala kamar na tukin mota da dai sauransu.

Wanda hakn yasa aka kamata aka yanke mata hukuncin shekara shida a gidan yari, sai kuma kotun daukaka kara ta yanke mata hukuncin shekara 34 yanzu kuma ba zata fita kasar waje ba har sai nan da wa’yan nan shekarun.

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta kama 'yan 'uwa uku a jihar Kebbi bayan sun kashe wanda suke zargi ya sace masu babur

Matar tanada yara guda biyu kuma dalibar PhD ce a jami’ar Landan dake garin Leeds, yayin da wata kawarta ta bayyana cewa matar bata taba tunanin cewa wannan abin datayi zai jawo mata wata matsala ba.

Kuma yanzu tanada kwanaki talatin da aka bata na daukaka kara izuwa kotun koli.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.