fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da hukuncin da ya wanke AA Zaura bisa zargin zambar $1.3m

Wata Kotun Daukaka Kara da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya ta yi watsi da hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya ta Jihar, wanda ya wanke mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2023, Abdulsalam Sale Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani AA Zaura bisa zargin zamba.

Kotun ta yi hukuncin ne ranar Laraba 13 ga watan nan na Afrilu.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC ce ta gurfanar da Zaura a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zarge-zarge biyar da suka shafi zamba cikin aminci.

EFCC t a zargi Zaura da yi wa wani dan kasar Kuwait zambar dala miliyan daya dubu dari uku da ashirin bayan ya yi ikirarin cewa yana harkar kasuwancin gidaje a Dubai, Kuwait da wasu kasashen Larabawa.

Karanta wannan  APC ta gaza domin shugaba Buhari bai damu da ilimin Najeriya ba, cewar daliban Najeriya

Wata sanar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce ranar 9 ga watan Yunin 2020, Mai Shari’a A. L Allagoa ya wanke Zaura wanke shi daga dukkan zarge-zarge.

Sai dai mai shigar da kara, Musa Isah, wanda bai gamsu da hukuncin ba, ya nemi Kotun Daukaka Karar ta soke hukuncin karamar kotun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.