fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kotun ECOWAS ta gargadi shugaba Buhari cewa kar ya sake rufe kafar sada zumunta ta Twitter

Kotun ECOWAS ta gargadi gwamnatin Najeriya cewa kar ta sake maimaita kuskuren data yi na rufe kafar sada zumunta ta Twitter a kasar.

Chief Malcolm Emokiniovo Omirhobo ne ya shigar da karan inda yace kulle kafar sada zumuntar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ya sabawa dokar jin dadi da walwalar al’umma.

Saboda haka ne kotun a yau ranar alhamis ta gargadi gwamnatin kasar cewa kar ta sake maimaita irin wannan barnar.

Shugaba Buhari ya bayar da umurni a rufe kafar sada zumuntar ne bayan sun goge wata magana daya yi na gargadi ga ‘yan ta’addan haramattaciyar kungiyar Biafra.

Leave a Reply

Your email address will not be published.