Babban kotun majistare ta jihar Ondo dake babba birnin jihar watau Akure, ta damke wani mutun da laifim yin lalata da yarinya yar shekara 15.
Kuma ta yanke masa hukuncin watanni 12 a gidan yari ba tare da bashi damar biyan kudin beli ba.
Inda mai gabatar da kara na kotun ya bayyana cewa mai laifin, Stephanus Stephen yayi lalata da yarinyar a lokuta da dama tsakanin watan febrairu zuwa mayu.
Kuma itana yarinyar ta bayyana hakan, inda tace yayi barazar kashe ne idan har ta sanar da wani.