Kotun Shari’ar musulunci dake Kano ta bayyana cewa ta mikawa babban lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana takardun matashi, Yahaya Aminu Sharifai da aka yankewa hukuncin kisa saboda kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Falana ya bukaci a bashi takardun shari’ar Yahaya ranar Talatar data gabata dan tsaya masa ya daukaka kuma a Yau, Alhamis, kotun ta ce ta mikawa wakilansa a Kano takardun Shari’ar.
Hakan na zuwane bayan da sauran kwanaki 7 kacal kwana 30 da aka baiwa Yahaya ya daukaka kara su kare.