Kotun magistare ta kasar Kenya ta yankewa dan Najeriya hukuncin kwanaki talatin a gidan maza bayan ya zagi budurwarsa.
Kotun ta caje Olaydaju ne da laifin kokarin tayar da hankulan al’umma a ranar 14 ga watan Yuli a Birnin Nairobi.
Kuma matashin ya zagi hukumar da buduwar tasa ta kaiwa karansa wanda suka kama shi suka maka shi a kotu ta yanke masa hukunci.
Amma ta bashi damar biyan diyya naira dubu talatin ko kuma ta kai shi gidan maza na tsawon kwanaki talatin.