Kotun Kolin Najeriya ta bai wa bangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje nasara a kan zabukan shugabancin jam’iyyar APC reshen Jihar.
Hakan na nufin bangaren tsohon gwamnan Jihar, Mallam Ibrahim Shekarau, ya sha kaye a shari’ar da aka soma bayan baraka ta kunno kai tsakanin bangarorin biyu sakamakon gudanar da zabuka daban-daban na shugabancin APC a Jihar ta Kano.
A wani hukunci da daukacin alkalai biyar da suka zauna a shari’ar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, suka yi a yau Juma’a, Kotun ta tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya halatta shugabancin bangaren Gwamna Ganduje.
Rikici ya barke ne bayan Sanata Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano sun balle daga bangaren Gwamna Ganduje suka kafa abin da suka kira G-7, inda suka zargi Gwamnan da rashin adalci a shugabancin APC.
Hakan ya sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na Jiha.
A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.
Wadannan zabuka sun raba kawunan ‘yan jam’iyyar ta APC a Jihar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya. Hasali ma, rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau sun rika yi wa juna shagube.
APC Maslaha: Wasu ‘yan jam’iyyar sun kafa sabuwar ƙungiya a Kano
Wasu ‘ƴan jam’iyyar APC a jihar ta Kano sun kafa wata sabuwar ƙungiya mai suna APC Maslaha.
Sabon ɓangaren dai na ƙarƙashin shugabancin Alhaji Aminu Dabo, wanda makusanci ne ga gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran jagororin ƙungiyar su ne Alhaji Kabiru Kama Kasa, da Alhaji Yusuf Ado Kibiya, da Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan Tama da Farfesa Mukhtar Ɗankaka a matsayin Sakatare.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ɓangaren su Malam Ibrahim Shekaru suka yi watsi da tsarin da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta bi wajen kafa kwamitin da ya yi ynuƙurin sulhu a watan Fabarairu tsakaninsu da Gwamna Ganduje, kan shugabancin jam’iyya a jihar.
Sai dai sabon ɓangaren na APC masalahar kamar yadda babban jami’i Alhaji Yusuf Ado Kibiya ya shaida wa BBC, su ba sa rigima da kowane ɓangare na APC a Kano, “kawai suna kokari ne su samar da daidaito a tsakanin ɓangarorin da ke jayayya da juna”.