fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Kotun Koli ta kori rokon hana kwace kudaden Abacha da iyalan sa suka nemi ta yi

Kotun Koli ta yi fatali da wani roko da iyalan Abacha suka shigar, inda suka nemi kotun ta hana gwamnatin Najeriya kwace makudan kudaden da tsohon shugaba na mulkin soja, Sani Abacha ya kimshe a asusun bankunan wasu kasashen waje.

Kudaden dai su na kimshe ne a asusun ajiyar Abacha da ke Ingila, Tsibirin Jersey, Liechtenstein, Luxembourg.
Babbar Mai Shari’a Binta Augie ta Kotun Koli ta karanto hukuncin kotun, inda ta kara jaddada wa Najeriya ikon kwace kudaden da kuma kulle asusun, hukuncin da Babban Mai Shari’a CC Nweze ta jaddada bayan da Kotun Daukaka ta yanke shi.
Kotun Koli ta ce iyalan Abacha ba su da hurumin da za su daukaka ko su yi ja’inja da hukuncin da Gwamnatin Najeriya ta yanke dangane da kudaden, tun cikin shekarar 1999.
Tun cikin 2005 ne Mai Shari’a A.T Liman ya yanke hukuncin kwace tulin kudaden wadanda Abacha ya kimshe tun a lokacin da ya yi mulki, 1993 zuwa 1998.
Daga nan ranar 16 Ga Fabrairu, 2005, Gwamnatin Switzerland ta maido wa Najeriya dala milyan 458 daga cikin dala milyan 508 na kudin.
Daga nan ne iyalan Abacha suka fara tsallen-badake daga wannan kotu zuwa waccan, su na neman kotu ta hana Najeriya kwace kudaden.
Shari’a ta yi tsawo har aka kai Kotun Koli, inda a karshe aka kara jaddada musu cewa kudi sun zama na ‘yan Najeriya.
Premiumtimeshausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Kalli bidiyo: Yanda magidanci ya lakadawa Fasto duka saboda yayi zina da matarshi


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.