fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kotun majistare a Jihar Kaduna, ta yankewa wani lebura hukuncin bulala 12 kan satar waya

Wata Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Talata ta ba da umarnin yiwa wani ma’aikaci dan shekara 23 mai suna, Shehu Abbas bulala 12 bisa laifin satar waya “Tecno” wadda darajarta ta kai kudi N56,000.

Abbas, mazaunin Kawo a jihar Kaduna, an gurfanar da shi a gaban kotu bayan ya amsa laifinsa tare da rokon a yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, yace wannan hukuncin zai kasance gargadi ga wadanda ke da aikata irin wadannan laifuka.

Emmanuel, ya kuma umarci jami’an kotun biyu da su yiwa mai laifin bulala 12.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *