An fara hukunta masu karya doka a kano
Bayan sanya dokar hana zirga-zirga a jihar kano. Gwamnatin jihar ta kafa kotun tafi da gidan ka wadda ke hukunta masu kunnan kashi akan dokar da gwamnati ta sanya na hana zirga-zirga a sakamakon bullar cutar corona jihar.
Tuni dai kotunan suka fara aiki a gurare daban daban a kwaryar birnin kano a ranar talata.
Inda aka rawaito kotun dake zaune a gadan kaya dake karamar hukumar gwale ta samu wasu da laifin fita ba bisa ka’ida ba, inda kotun ta hukunta wani mai suna Sani Usman, wanda ya bayyana cewa “Naje ne in siyo Gas din abinci aka kamani. Injishi
Kotun dai tai masa tarar Naira dubu 2 Wanda nan take ya biya aka salla me shi.