Kotun majistare ta jihar Bauchi ta yankewa wani direban mota mai suna Samaila Hamisu Garba hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin wani jami’in hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).
An gurfanar da mai laifin ne biyo bayan wani hari da aka kaiwa ma’aikacin FRSC a bakin aiki da kuma tukin mota mai hatsari mai lamba FRSCBH/01/22, FRSC vs Samaila Hamisu Garba.
Sai dai kotun ta bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar Naira 40,000 da ya biya wa kotun.
Kotun ta kuma umarce shi da ya biya diyyar kudi N20,000.00 ga ma’aikatan FRSC da aka ci zarafinsu tare da raunata su.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Kwamandan hukumar FRSC reshen Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya yaba wa kotun bisa gaggauta hukuncin da ta yanke, inda ya ce zai zama darasi ga wasu da ke iya yin irin wadannan ayyuka.