fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Koulibaly ya haskaka yayin da Chelsea ta raba maki da Tottemham bayan sun tashi wasa da kunnem doki 2-2

Kungiyar Tottenham da Chelsea sun tashi wasa da kunnen doki a wasan da suka buga na gasar firimiya a yau ranar lahadi 14 ga watan Augusta.

Chelsea ce ta fara jagoranci a wasan inda kwalliya ta biya kudin sabulu domin sabon dan wasan baya data dakko daga Napoli, Kalidou Koulibaly ne yaci mata kwallon.

Kafin Højbjerg ya ramawa Tottenham kwallon sannan Reece James ya kara ciwa Chelsea guda.

Duk da haka dai a karshe raba maki sukayi domin zakaran gwajin Spurs Harry Kane saida ya kara ciwa tawagar Antonio Conte kwallo guda.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.