Manchester City ta cigaba da jagoranci da maki maki uku a saman teburin gasar Firimiya bayan ta lallasa Newcastle daci 5-0 kuma Liverpool ta barar da maki, yayin da wasanni uku suk rage wannan kakar.
Yayin da Manajan Manchester City, Pep Guardiola yayi tsokaci akan babbar kungiyar adawarsu watau Liverpool, wadda ta tashi wasa daci 1-1 tsakaninta da Tottenham a ranar asabar.
Pep Guardiola, yayin ganawa da manema akan nasarar daya yi na cigaba da zama a saman teburin yace, kowa a Ingila Liverpool yakeso ta lashe kofi hatta manema labarai, amma abin na tafiya ne yadda ya kamata.