Tuesday, October 15
Shadow

Kowane Musulmi Imaninsa Yana Cika Ne Idan Ya Yarda Tare Da Rungumar Kowace Irin Kaddara Ce Ta Same Shi, Cewar Sarki Sanusi II A Hudubarsa Ta Yau Juma’a

Daukar ƙaddara mai kyau ko mara kyau yana daga cikin cikar imanin mutum -inji Sarki Sanusi a huɗubarsa ta yau Juma’a

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda zai iya tuhumar Allah dangane da ƙaddara. Sabon sarkin ya faɗi hakan ne yayin huɗubar sallar Juma’a a masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano.

Huɗubar dai ta mayar da hankali ne kan imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau.

” Duk wanda ya yi imani da Allah shi kaɗai to dole ne ya yi imanin duk abin da Allah ya ƙaddara. Ba a tambayar ubangiji dalilin aiwatar da al’amura.

Karanta Wannan  Mai martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin yan Majalisar dokoki na Jahar kano tsagin jam’iyyar APC, sun kawo ziyara tare da jaddada mubayi’ar su

An faɗa mana cewa duk wanda bai yarda da ƙaddara ba cewa daga Allah take, imaninsa bai cika ba. Ya kamata mu zama masu godiya ga Allah a yanayi daɗi ko wuya. Dole ne mu yarda cewa duk abin da ya faru a gare mu ta ƙaddara ce daga Allah, sannan abin da ba mu iya samu ba shi ma daga Allah ne.” In ji Sarki Sanusi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *