Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya umarci ma’aikatan gwamnati a jihar da su bayyana kadarorin su ko kuma su fuskanci fushin hukuma kamar yadda dokokin kasa suka tanada kan rashin bayyana kadarorin.

Ya ba da wannan umarnin ne a ranar Talata a lokacin da aka fara wani taron bita na kwana biyu a kan tsananin bin kadin bayanin kadara da ka’idojin da’a na jami’an gwamnati wanda kotun ma’aikata ta shirya.
Ya ce umarnin ga jami’an gwamnati a jihar don su bayyana kadarorinsu ya zama dole, kuma a hada kai da manufar gwamnatinsa na cusa koyar da kula da kudi da kuma kula da dukiyar jama’a cikin tsanaki.
Ya bayyana taron bitar a matsayin mai dacewa, a kan lokaci, kuma mai matukar mahimmanci kamar yadda zai cusa zukatan jami’an gwamnati kyawawan halaye na aminci da rikon amana yayin gudanar da ayyukansu daban-daban.