Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike yayi kira ga magoya bayansa na jam’iyyar PDP dake jihar cewa su cigaba da goyon bayan jam’iyyar dari bisa dari.
Gwamnan yayi kiran ne mako guda bayan da tasohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya doke shi a zaben fidda gwani.
Inda mataimakinsa Ipalibo Harry-Banigo ya wakilce shi wurin isar da sakon na mika godiyarsu na goyon bayan jam’iyyar a zaben fidda gwanin da suka gudanar cikin limana.
Yace magoya bayan jam’iyyar kar suyi kasa agwiwa su cigaba da goyon bayan PDP ta lashe zaben shekarar 2023 duk da ya fadi zaben fidda gwani, domin jam’iyyar a shirye take ta ceto Najeriya a halin datake ciki.