Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa, shine mafi cancantar zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.
Wike ya bayyana cewa, yana karfi, kwarewa da basirar da zai iya zama shugaban Najeriya dan haka yana neman a bashi damar hakan.
Ya bayyana hakane a jihar Gombe inda ya kai ziyarar neman tuntuba kan tsayawa takarar tasa.