Kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere ta baiwa gwamnonin Arewa shawarar su dauki matasa aikin samar da tsaro.
Sakataren kungiyar, Sola Ebiseni ne ya bayar da wannan shawara inds yace gwamnan Kaduna dake maganar dauko sojojin haya ba itace mafita ba.
Yace babu wasu sojojin haya da zasu iya magance matsalar tsaron da ake fama da ita.
Yace asalima gwamna El-Rufai da sa o insa sauran gwamnonin yankin ne suka taimaka wannan matsalar ta ta’azzara.
Yace maganar yin Allah wadai da aikin sojojin Najeriya sam bai dace ba, abinda ya kamata shine kawai a kafa rundunar tsaro wadda zata taimakawa sauran jami’an tsaron wajan tabbatar da zaman Lafiya.