Ministan Lafiya, Osagie Ehanire yayi gargadin cewa lura da ‘yanda ‘yan Najeriya basa bin dokokin dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19, cutar ka iya dawowa nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Legas. Yayi kira ga gidajan yada labarai da su rika yada ka’idojin da ya kamata abi wajan kaucewa cutar Coronavirus/COVID-19.
Yace ka’idojin sune wanke hannu, Nesa-nesa da juna da kuma saka takunkumin rufe baki da hanci.
“I fear that with the laxity displayed by our own population, our own second wave is imminent.”