Me magana da yawun shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Femi Adesina ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya ya kamata su godewa Allah suna samun abincin da zasu ci a gida Najeriya ba sai an fita nema kasashen waje ba.
Adesina ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook inda yace ‘yan Najeriya ya kamat su godewa Allah suna samar da abincin da suke ci a cikin gida Najeriya.
Yayi magana akan taron da shugaba Buhari yayi da shugaban bankin raya nahijar Africa AfDB watau Akinwunmi Adesina.
Yace Adesina ya bayyana yanda yakin kasar Rasha da Ukraine ya tayar da farashin Alkama dana takin zamani.
Ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su koma gona.