fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ku Gudanar Da Gajeriya Huduba A Sallar Idin Bana>>Gwamna Ganduje Ga Malamai

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya shawarci malaman addini a Kano da su gabatar da gajeriyar huduba yayin sallar idi.

 

 

A wata takarda da sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a jiya, ya ce za a yi sallar idi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar. Amma dole ne Musulmai su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka tanadar don sallar jam’i.

 

“Kamar yadda manyan Malamai suka shawarci limamanmu, ya kamata a yi huduba gajera a yayin sallar Idin saboda kalubalen Corona virus da muke fuskanta”.

Karanta wannan  Matafiyan babbar Sallah a jihar Kaduna sun koka kan tsadar kudin mota

 

 

Ya ce akwai bukatar jama’a su hanzarta watsewa ana kammala sallar sannan su ci gaba da kiyaye dokokin kiwon lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.