fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ku kamani in kun isa>>Gwamnan Bauchi ya gayawa EFCC

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya kalubalanci hukumomin yaki da rashawa da suka hada da EFCC da sauransu cewa su kamashi idan sun isa.

 

Gwamnan ya bayyana cewa idan suna da hujjar cewa, yana satar dukiyar gwamnatin ne ko kuma yana rashawa su fito da hujjar.

 

Gwamnan ya bayyana hakane yayin ganawa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP din.

 

A shekarar 2017 ne dai EFCC ta gurfanar da Sanata Bala wanda tsohon ministan Abuja ne a gaban kotu kan zargin Almundahanar Miliyan dari 864.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada sabuwar mai bashi shawara akan harkar siyasa

 

EFCC tace ya samu kudinne a matsayin rashawa da aka bashi kan wasu filaye lokacin yana ministan Abuja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.