fbpx
Thursday, August 18
Shadow

KU KARANTA KU KARU: Sunnoni Da Ladubba Guda 17 Na Ranar Idi

*1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi*

Saboda Hadisn Umar bin kaddhaba R.A.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 948.

*2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi*

Ibn Umar R.A ya kasance ba ya fita sallar idi har sai ya yi wankan idi.
@ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ، 384.

Sa’id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*”Manyan sunnonin ranar Idi guda uku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin a fita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi”*
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ‏( 3/104 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

*3-Yin sallar idi kafin Huduba*

Manzon Allah SAW da Abubakar da Umar sun kasance suna yin Sallar idi kafin Huduba.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ – ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ-ﺗﻔﺮﻳﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :972 ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻰ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻰ ﺩﺍﻭﺩ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 1134 0

*4-Haramun ne yin Azumi a ranar Idi guda biyu, idin azumi da idin Layya*

Manzon Allah SAW yana cewa:
*(Babu azumi a ranakun idi guda biyu,idin azumi da idin Layya)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ،1197

*5-Cin abinci ko wani abu kafin tafi sallar idin azumi, kuma an fi so a ci dabino. Idan idin layya ne ana kamewa ba acin komai sai an dawo daga Idi*

Manzon Allah S.A.W ya kasance ba ya tafiya sallar idin azumi har sai ya ci Dabino.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 953.

*6-Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba*

Manzon Allah SAW ya kasance yana fita musalla ne don yin sallar idi.
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 510.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*”Manzon Allah S.A.W yana fita ne da wuri zuwa musalla dan yin sallar idi….”*
@ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، 1294

*7-Sunna ne a fitar da mata da yara zuwa sallar idi, amma matan su yi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshin sa yake tashi*
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 511.

Sayyadina Abubakar R.A yana cewa:
*”Hakki ne akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi”*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ .

*8-Tafiya masallacin idi a kasa idan da ikon hakan*

Manzon Allah SAW ya kasance yana tafiya masallacin idi a kasa kuma ya dawo a kasa.
@ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 1078 ‏( 1311 )

Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa:
*”Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma a ci wani abu kafin a fita idi”*.
@ﺣﺴﻦ /ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 530

*9-Canza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi*

Manzon Allah SAW ya kasance yana canza haryar dawowa daga masallacin idi.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 986.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*”Na koya daga Manzon Allah SAW canza hanya har dawowa daga masallacin idi*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 254.

*10-Yin kabarbari na ranar Idi*

*_Ana fara kabbarar ne daga faduwar ranar karsen ta Ramadhana idan an ga watan Shawwal za a fara yin kabbarori har zuwa fitowar LIMAN dan yin sallar IDI_*

Imam Sun’ãni yana cewa:
*”Yin kabbar tun daren idi har zuwa fara sallar idi yin hakan sunna ce a bisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin Allah Madaukakin Sarki*-
*(ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ )*
@ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185
@ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ : 100-101 .

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

*11-Sigogin Kabbarorin ranar Idi*
Daga cikin sigogin da aka samo daga Sahabbai sun hada da;-

Siga ta farko;-
*ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺃﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*
@ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ.ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ‏( 3/125 ‏)ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

Siga ta biyu;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*

Siga ta Ukku;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﺃﺟﻞ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻧﺎ .
@ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ
‏( 3/125 ‏)ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ

*12-Sanya Turare dan zuwa sallar idi*

Abdillahi dan Umar R.A ya kasance ba ya fita sallar idi har sai ya yi wanka ya sanya turare.
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ – ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻓﻲ ﺍﻻﻏﺘﺴﺎﻝ ﻟﻠﻔﻄﺮ ﺣﺪﻳﺚ 015

*13-Ba a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta, kuma ba a kiran sallah ko ikama*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :1517
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ – ﺑﺎﺏ ﻣﺎﺭﻭﻱ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺻﻼﺓ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻻﺑﻌﺪﻫﺎ ﺣﺪﻳﺚ 0143

*14-Yin gaisuwar sallah da fatan lkairi da fatan Allah ya maimata mana*

An samu daga aiyukan magabata suna yi wa junansu barka da sallah da fatan alkairi, daga cikin abinda suke fada akwai;-
*ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ*

*15-Yin wasa na al’ada wanda babu sabon Allah a cikin sa dan nuna farin ciki ranar Sallah, sannan mata za su yi nasu wake da buga kayan kidansu na al’ada wanda babu sabon Allah*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ – ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ – ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺤﺮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺪﺭﻕ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ – ﺣﺪﻳﺚ :921 ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ – ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ – ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ – ﺣﺪﻳﺚ 01527:

*16-Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi*

Manzon Allah SAW ya kasance ba ya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara ci ne daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa.
@ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ / .144

*17-Girmama ranar Idin layya akan sauran ranaku domin ranace mai girma awajan Allah*

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Mafi girman ranaku a wajen Allah sune; Ranar Layya da ranar washe garin Layya)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

Allah ne mafi sani

Don Allah ƴan uwa kada ku yi wa sauran ‘yan uwa rowa ku yada (sharing) don su gani su amfana da ku.

Ina yi wa dukkan musulmai barka da sallah da fatan alkair, Allah ya maimata mana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.