fbpx
Saturday, June 10
Shadow

“Ku kwantar da hankulanku kwanan nan zamu ceto maku ‘yan uwanku dake hannun ‘yan bindiga”>> Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Shugaban kasa mejo janar Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin Najeriya dasu gaggauta ceto mutanen da ‘yan bindiga sukayi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna.

Hadimin shugaba Buhari ne ya bayyana hakan, watau Garba Shehu inda yace shugaba na maraba da mutane 11 da aka ceto suka koma ga iyalansu.

Kuma suma sauran kwanan nan zasu koma gidajensu saboda haka iyalansu su kwantar da hankulansu za’a ceto masu masoyansu da kuma ‘yan uwansu.

A ranar 28 ga watan maris na wannan shekarar ne ‘yan bindiga suka kai hari jirgin kasa a Kaduna wanda ke dauke da fasinjoji 970, suka kashe mutane tara sukayi garkuwa da sama da mutane 60.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *