Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana harin da aka kau karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija a matsayin cin zarafi ga Najariya wanda yace ba za’a bari ya tafi hakanan ba.
Shugaban ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a wajan harin wajan tunkarar ‘yan Bindigar.
Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.
Yace auna girmama sojojin Najariya musamman wadanda suka rasa rayukansu wajan yaki da ta’addanci.
Yace amma ba za’a taba bayar da kai ga ayyukan ta’addanci su yi nasara akan Najariya ba.
Shugaban yace duk inda ‘yan Bindigar suke sai an kwakulosu an kashesu kuma wannan harin ba zaisa jami’an tsaro su yi kasa a gwiwa ba.