Kungiyar Liverpool ta dare saman teburin gasar Fimiya bayan ta doke Manchester United daci 4-0 a gida.
Liverpool taci kwallayen ne ta hannun Luiz Diaz da Mohammed Salah wanda yaci biyu sai Sadio Mane, inda ita kuma United tayi kewar tauraronta Ronaldo wanda bai buga wasan ba sanadiyyar mutuwar yaronsa.
Bayan an tashi wasan kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewa hankalanshi gabadaya yana wurin Ronaldo da iyalansa yayin da ake buga buga wasan saboda rashin da yayi na yaronsa.
Inda ya kara da cewa akwai abubuwa muhimmai da sukafi wasan tamola a rayuwa kuma rai na daya daga cikin su, kuma yaji nasarar da sukayi a wasan.