Ministan yads labarai da Al’adu Alhaji Lai Muhammad ya jawo hankalin ‘yan Najeriya akan su riga godewa Allah a duk halin da suka tsinci kansu.
Lai Muhammad ya ce ba wai lallai sai mutum yayi kudi bane sannan zai rika godewa Allah ba.
Yace a duk halin da mutum ya samu kanshi ya rika godewa Allah.
Sannan ya kuma jawo hankalin iyaye su rika baiwa ‘ya’yansu tarbiyya ta gari.