fbpx
Monday, October 26
Shadow

Ku rika kokari kuna cin abinci me gina jiki saboda zai rika baku kariya daga Coronavirus/COVID-19>>Gwamnati Baiwa ‘yan Najeriya Shawara

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da abinci mai gina jiki a matsayin wani babban bangare na dabarun hana ci gaba da yaduwar COVID-19 da gina karfin gwiwar mutane da al’ummomi.
Gwamnatin ta kuma jaddada bukatar ba da fifiko ga kasafin kudin da ake warewa bangaren noma da samar da abinci a kasar.
Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ce ta bayyana hakan a Abuja a ranar Juma’a a wani shiri da kungiyar Action Against Hunger (Nigeria) da kungiyar masu jaddada kayan abinci masu gina jiki a Najeriya suka shirya don tunawa da ranar abinci ta duniya.
Tallen, wanda Darakta (Ci gaban Yara) ta wakilta a ma’aikatar, Jummai Mohammed, ta ce kiran ya zama wajibi saboda kalubalen da ke fuskantar Najeriya a yanzu.
Ta ce cutar ta COVID-19 da ke yaduwa ta gurgunta harkokin rayuwa kuma ta karu ta kowane fanni, musamman ga mata.
Tallen ta ce wani rahoton da ke akwai wanda Nijeriya ta nuna shi ne na kan gaba a yawan yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a duniya, inda sama da miliyan biyu da rabi ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *