Daga Muryoyi
Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya ja kunnen iyaye su koyar da ya’yansu tarbiyya da hali nagari da kyakkyawan mu’amala don guje yin furuci ko kalaman rashin daraja da ka iya jawo fitina.
Gwamnan ya nemi jama’a su rika mutunta addini da al’adun juna da nisantar cin mutuncin addini ko al’adar kowa ta kowane hali.
El-Rufai ya yabawa Jami’an tsaro da Malaman addini da Limamai da Sarakuna bisa yadda suka tashi tsaye wajen fadakar da jama’a don ganin rikicin da ya faro a wata jiha dake Arewacin Najeriya bai fallasu ba.