Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa, ya kamata iyaye su rika saka ‘ya’yansu mata a aikin soja.
Me baiwa gwamnan jihar ta Yobe shawara akan tsaro, Janar Dahiru Abdulsalam ne ya bayyana haka.
Yayi kira ga ‘yan jarida dasu rika wayarwa da iyaye kai game da saka ‘ya’yansu mata aikin soja.
Ya bayyana cewa, addini da al’ada na hana iyaye saka ‘ya’yansu mata aikin soja a jihar.