Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ‘yan Najariya su saka ido da tabbatar an yi zaben gaskiya a shekarar 2023.
Shugaban ya bayyana hakane a sakonsa na karshen shekara da ya fitar.
Yace gwamnati zata yi kokarin ganin an yi zaben gaskiya da kuma dakile duk wani yunkurin yin magudi.
Shugaba Buhari ya nemi mutanen Najariya da su saka hannu wajan taimakawa gwamnatin ganin an yi sahihin zabe