fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ku saka kasar Ukraine a addu’a Allah ya basu zaman lafiya>>Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da Duniya baki daya, musamman Musulmai dasu yi amfani da Azumin watan Ramadana da ake ciki wajan saka kasar Ukraine a addu’ar samun zaman lafiya.

 

Yace yakin na kasar Ukraine ya dade kuma an kashe mutane da yawa, yace kuma yana barazana ga zaman lafiya da kuma bangaren abinci.

 

Shugaban ya bayyana hakane a fadarsa yayin ganawa da wakilan diplomasiyya a shan ruwan da ya shirya musu da yammacin ranar Alhamis.

Karanta wannan  Na kusa da Buhari na ta kokarin ganin Tsohon Shugaban kasa, Jonathan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a APC

 

Shugaba Buhari ya kuma jawo hankalin kasashen waje da cewa su kiyaye kada su rikawa Najeriya katsalandan a harkar zabe.

 

Shugaban ya kuma bayyana cewa sun samu nasara sosai a yaki da Boko Haram inda kuma ya jinjinawa jami’an tsaro kan nuna kwazo da suke a yaki da ta’addanci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.