fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Ku sake Tunnani game da Barin Jama’a su yi walwala>>Gwamnatin Taraya ga jihohi

Gwamnatin tarayya ta ja hankalin jihohin Najeriya da suka sassauta dokar hana zirga-zirga duk da yawan masu kamuwa da cutar Coronavirus/COVID-19 dake karuwa.

 

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne yayi wannan kiran a wajan ganawar da kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 da yake jagoranta yayi da manema labarai.

Jihohin Kano, Zamfara,  Bauchi, Cross-River,  Nasarawa da sauransu na daga cikin wanda suka saukaka dokar zaman gidan inda harma wasu suka bada damar a ci gaba da Ibada amma a kiyaye dokokin da kwarrun masanan Lafiya suka bayar.

 

Yace yana da kyau jihohi su fahimci cewa sassauta dokar hana zirga-zirga ta hanyar da zata maida hannun agogo baya kan nasarorin da aka samu matsalane.

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

 

Yace dokar hana mutane sama da 20 taruwa a guri daya ya kamata ace an ci gaba da dabbakata.

 

Yace dan haka yana kira ga jihohin da su sake nazarin matakan da suka dauka na sassauta dokar.

 

Ya kuma bayyana damuwa kan yanda masu kamuwa da cutar ke karuwa a Fadin Duniya inda yace cutar zata shafi yanda muke gudanar da rayuwarmu na tsawon Lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.