Shugaban kasar Najeriya, Mejo Janar Muhammadu Buhari ya umuci dakarun sojin Najeriya dasu shafe tarihin ‘yan ta’adda a kasar.
Shugabam ya bayyana hakan ne a ziyarar daya kai jihar Kaduna yau alhamis yayin da Jaji ke bikin yaye daliban sojojin da suka kammala makaranta.
Inda ya jinjina masu dama sauran dakarun soji bakidaya kuma ya umurce dasu kawo karshen ta’addanci a kasa Najeriya.
Shugaban kasar ya kara da cewa Najeriya na fuskantar matsalar tsaro ta ‘yan Boko Haram, ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane saboda haka ya kamata su daure damara.