fbpx
Friday, January 15
Shadow

Ku shirya ma mafi munin yanayi akan Cutar Coronavirus/COVID-19>>Gwamnatin tarayya ta gayawa ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘ya  Najeriya da shi zauna cikin shirin komi na iya faruwa akan cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Da yake magana a babban birnin tarayya, Abuja,Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya da sauran ‘yan Najeriya ya kamata su kara fahimtar cutar da kyau.

 

Yace dolene su ma’aikatan jinya su ci gaba da sadaukar da kansu wajan yin aiki yanda ya kamata amma fa duk da haka sai an shiryawa mafi munin matsayi.

 

Yace a kullun suna kara fahimtar yanatin cutar kuma dan haka dolene su ci gaba da daukar matakan da suka dace.

 

Yace abin takaici hadda manyan Mutane a cikin masu baiwa kansu magunguna idan sun ji yanayin rashin lafiya, yace hakan ya taimaka sosai wajan yawan mace-macen da aka samu a kasarnan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *