Kungiyar ‘yan kasuqar Man fetur maau zaman Kansu, IPMAN ta baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa su shirya sayen man Fetur din da tsada.
Sun bayyana cewa farashin Man fetur din zai iya kaiwa Naira 195 akan kowace Lita.
Sun kuma zargi rashin matsaya daga gwamnatin kan sakarwa kasuwa gudanar da farashin man fetur din.
NNPC a makon da ya gabata ta ce babu maganar kara kudin Man fetur sai ta gana da ‘yan kungiyar Kwadago.
A bangaren kungiyar kwadagon kuwa tace ba zata ce komai ba tukuna sai an kara farashin man.