fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Ku shirya shan mamaki akan sakamakon binciken Magu>>Gwamnatin tarayya ta gayawa ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya da cewa su karkada kunnuwansu su shirya shan mamaki akan sakamkon binciken Magu da zai fito nan bada dadewa ba.

 

Me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da gidan Talabijin din Channelstv.

Yace kwamitin da ya binciki Magu ya kusa kammala rahoton da zai fitar kuma ga dukkan alamu lamarin zai baiwa ‘yan Najeriya mamaki sosai.

 

Ya kara da cewa ‘yan Najeriyar kada su kula masu sukar binciken Magun, yace lamarin binciken Magu zai jawowa gwamnatin shugaba Buhari abin kunya amma daga baya za’a wanke ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.