fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Ku tabbatar da cewa kun kama ‘yan ta’addan da suka kaiwa gidan kuekukun Kuje hari, Tinubu ya fadawa gwamnatin tarayya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya nemi gwamnatin tarayya data tabbatar da cewa ta kama ‘yan ta’addan da suka kai hari gidan kurkuku na Kuje.

A ranar talata ne ‘yan ta’addan suka kai harin a babban gidan kurkuku dake babban birnin tarayya Abuja, kuma ‘yan gidan kurkuku da dama sun tsere abinsu.

Hadimin Tinubu, Tunde Rahman ne ya bayyana hakan inda yace Tinubu ya kara da cewa suma wa’yanda suka tsere dole a kamo su.

A jiya ne Tinubu ya dawo gida Najeriya daga kasar Faransa bayan yaje meman shawara kan zaben shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.