Babban Faston cocin RCCG, Enoch Adeboye ya bayyana cewa, kiristoci su tashi su kare kansu dana matsalar tsaron da ake fama da ita.
Yace babu inda addininsu ya hanasu tashi tsaye dan kare kansu.
Ya bayyana hakane a wajan tarin cocin da yayi inda yace ya duba baibul kaf babu inda aka hana kiristoci kare kansu.