Tsohon shugaban kasar Najeriya, Okusegun Obasanjo ya nemi matasan Najeriya cewa su tashi tsaye su ansa mulkin kasar a hannun tsaffi.
Inda yace su daina bari ana ce masu matasa manyan gobe idan har basu tashi tsaye ba goben ba zata taba zuwa ba, saboda haka yanzu ce goben.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin dayake tattaunawa da dan wasan tamola na Najeriya, Segun Odegbami ranar asabar.