Shugaban kasar Najeriya, Majo Janar Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin APC dasu taya shi zabar wanda zai maye masa gurbinsa a shekarar 2023.
Buhari ya bayyana masu hakan ne a taron da suka gudanar a jihar Abuja a Aso Rock, wanda shugaban APC Abdullahi Adamu ya halatta.
Kuma Buhari ya kara da cewa yana so jam’iyyar ta samu cigaba sosai ba wai na hadin kai kadai ba, yanaso su cigaba da mulkin kasa Najeriya da kuma jihohinta bakidaya.