fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ku yi hakuri, mun yi iya bakin kokarinmu>>Ighalo ya gayawa ‘Yan Najeriya: Najeriya ce kasar da ta fi bamu wahala>>Mahrez

Labarin wasanni ya bayyana cewa, Tauraron dan kwallon kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Odion Ighalo ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri akan rashin nasarar da suka yi jiya a hannun kasar Algeriya da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Afrika dake ci gaba da gudana a kasar Egypt.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Labarin wasannin sun ci gaba da cewa, Ighalo da yake hira da manema labarai bayan wasan na jiya yace, ‘yan Najeriya ku yi hakuri, Wasane me wahala kuma bamu da sa’a. Bayan da aka dawo hutun rabin lokaci mun yi wasa sosai amma ba’a samu yanda ake so ba. Zamu ko yi darasi daga kuskuren da muka yi da kuma neman matsayi na 3.
Ana kusa da hura tashine dan wasan kasar Algeria, Riyad Mahrez ya ci Najeriya kwallo daga bugun tazara wanda ya bayar da sakamakon wasan 2-1, kamar yanda labarin wasanni suka nunar.
Shima Mahrez din da yake hira da manema labarai bayan wasan yace, ‘yan kwallon Najeriya sun yi wasa me kyau, wasan da muka buga dasune wasan da yafi bamu wahala a wannan gasar,injishi.
Labarin wasanni ya ci gaba da cewa, Najeriya da Tunisia zasu buga wasan neman matsayi na 3 a gasar ta cin kofin Nahiyar Afrika a ranar Laraba me zuwa.
Sai kuma Senegal da Algeria zasu buga wasan karshe na daukar kofin Afrikan ranar Juma’a me zuwa idan Allah ya kaimu

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

Leave a Reply

Your email address will not be published.